Countdown
Connect with us

Labarai

ZANGA-ZANGA: Wanan shine matakin farko na shirye-shiryen NLC kan kawo karshen yajin aiki – Dr Silas Amos

Published

on

Dr Silas Amos yayin tataunawa da manema labarai a gurin zanga zanga NLC Hoto: channels tv Asali: channels tv

Ciyama din kungiyar malaman Jami’oi rashen Jami’ar Kaduna (KASU), Dr Silas Amos, ya bayana zanga-zangar da ke gudana a matsayin matakin farko na kungiyar kwadago NLC domin kawo karshen yajin aikin ASUU.

Amos ya bayana hakan ne a yayin ganawa da manema labarai a ranar talata a Kaduna, yayin zanga zangar da NLC ta shirya.

Ya Kara da zargin gwamnatin taraya da nuna rashin kulawa tare da kin cika alkawarin yarjejeniyar ta da kungiyar malaman jami’oi ASUU na shekarar 2009.

“Mun taru a nan a yau saboda ma’aikatan ilimi muma membobin kungiyar kwadago ne, babbar kungiyar da ke da alhakin hadakar kwadago a Najeriya wada itace kungiyar kwadago ta kasa ” inji shi.

“Mu rashen Kungiyar Kwadago ta Najeriya ne, bayan kungiyar ta gana ta gano cewa da yawa daga cikin mambobinta na cikin wahalhalu kuma wannan abu ya dade. Tsawon watanni shida da suka gabata an rufe jami’o’i saboda haka.

“Sun ga ya zama dole mu fito mu fahimtar tare da nuni da cewa kasancewarmu a cikin su, da kuma wahalar da iyayen wadannan daliban suke ciki, ya kamata a matsa wa gwamnati ta dauki matakan da suka dace don yin abinda ya kamata .”

Da yake Karin haske yace, matakin da ASUU ta dauka abu ne wanda bazai faruba inda gwamnatin tarayya ta cika dukkan yarjejeniyoyin da ta kulla da malaman jami’o’in.

ya yi gargadin cewa ma’aikatan Najeriya za su sanar da rufe harkokin hada-hada kasar baki daya idan har gwamnatin tarayya ta gaza shawo kan matsalar ASUU. da wuri-wuri.

Zafafa Labarai