Countdown
Connect with us

Labarai

Zanga-zanga: Abun kunya ne ace kasar dake yin kasafin kudi daya kai triliyan 16 ta kasa warware matsalar illimi – Shehu Sani

Published

on

Tsohon Sanata kaduna ta tsakiya, kwamured Shehu Sani, ya bayana cewa baban abin kunya ne ace kasar dake kasafin kudi da yakai kimani triliyan goma Sha shida ta kasa shawo Kan matsalar harkar illimi a Nijeriya.

Sanata Sani, ya fadi hakan ne a gurin gangami zanga-zangar kawo karshen yajin aikin malaman jami’oi dake gudana a baban birnin taraya Abuja, a yau laraba.

Ganagami na daga cikin matakin farko da hukumar kwadago ta kasa ta shirya don ganin Gwamnati ta dauki matakin kawo karshen yajin aikin ASUU.

A yayin jawabi Sanata Sani yace, ” Tun daga kan shugaban kasa, mataimaki Shugaban kasa, har da mafiya yawan Gwamnoni, Sanatoci, Yan majalisar taraya da na jihohi, ciyamomi dake Kan mulki a Nijeriya, dukan su sun afana da illimi makarantu gwamnati ne.

” Akwai abin kunya ace kasar dake kasafin naira triliyan sha shida ta kasa bunkasa bangaren illimi .

Ya kara dacewa wanan gangami shine farkon mataki na nuna ma gwamnati cewa sai tayi abinda yakamata.

In za a tuna kungiyar malaman jami’oi ASUU ta fara yajin aiki ne tun ranar 14 ga watan Faburairu, 2022.

Wanda kimani watanin biyar kenan har yau gwamnati bata shawo Kan matsalar ba, wanda yayi sanadiyar sa dalibai zama a gida.

Zafafa Labarai