Countdown
Connect with us

Siyasa

Zan Sauya Manufofin APC Idan Aka Zabe Gwamnan Kaduna – Ashiru

Published

on

Dan takara kujera Gwamna Jihar Kaduna a inuwar jam’iyyar PDP, Rt. Hon. Isa Ashiru Kudan, ya sha alwashin sauya manufofin mulki jam’iyar APC a Jihar Kaduna, matukar aka zabe shi a 2023.

Bayanin hakan na kunshe ne a wata sanarwa dauke da sa hanu Yakubu Lere El-Saed, Darekta hulda da Jama’a na kungiyar kampe din Isa Ashiru.

Ashiru, ya tausayawa kungiyar NUT rashen Jihar Kaduna, bisa korar mambobin ta sama da 2000, ya Kara dacewa zai sauya manufofin akan batun illimi da mulkin jam’iyar APC ta kawo, matsawar yaci zabe.

Sanarwa na kalubalantar dan takara kujera Gwamna na Jam’iyar APC Sanata Uba Sani, da ya fito ya fadi matsayin sa Kan batun korar Malamai da Gwamnati maici tayi, tare da shirin rushe kasuwar Gwari dake Rigasa tare da Kuma wata kasuwa a karamar hukumar Saminka.

Zafafa Labarai