Countdown
Connect with us

Illimi

Za a fara rabawa sabin malaman Sekondari 7600 takardun gun fara aiki, bayan shafe wata 10 da daukan su aiki

Published

on

Sabin malaman Sekondari da aka dauka aiki wata goma da suka wuce a fadin Jihar Kaduna, za su fara karban takadun gun fara aikin su aiki.

Rohotonin na bayana cewa batun raba musu gun aiki ya biyo bayan umarni da aka samu ne a ranar 9 ga watan Mayu, 2022 a gurin taron Kaduna Executive Council.

Inda aka umurci cewa ” a rabawa sabin malaman Sekondari da aka dauka aiki takardun gurin fara aiki a dukan ninwata makarantu Sekondari da ke fadin jihar Kaduna, a cikin kwana bakwai.”

A watan Janairu, 2019 ne aka gudanar da jarabawar daukan aiki ga wanda suka nema aikin koyarwa da adadin su ya Kai 62,000.

Inda hukumar kulada da Malamai na jihar Kaduna, (Kaduna State Teacher Board), ta tan tace mutum 14,000 wanda a cikin su ne a ka zabi malai 7600.

A ranar 19 ga watan Yuli, 2021 ne a ka raba ma malaman takardan daukan aiki, wanda wasu da dama daga cikin malaman har sun cire rai da aikin sabida shafe watanin ba albashi ba gun aiki.

Zafafa Labarai