Countdown
Connect with us

Siyasa

‘Ya’yan Honarabul Sani Sha’aban 17 Sun Siya Masa Fom Din Takarar Gwamna Jihar Kaduna A Jam’iyar APC

Published

on

‘Ya’yan tsohon dan majalisar wakilai, Honarabul Sani Muhammed Sha’aban 17 a ranar Alhamis suka sayawa mahaifinsu fom din tsayawa takarar gwamnan jihar Kaduna a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Da take yiwa manema labarai jawabi jim kadan bayan karbar fom din mahaifinsu daya daga cikin ‘ya’yan Sha’aban, Asmau Sani Sha’aban ta ce mu 17 yaran shi ne muka bayar da gudunmuwar N50m na ​​siyan fom din.

Sani Sha’aban ya sai fom din takara Gwamna a kaduna Hoto: Ahmad Tijjani Ramalan. Asali: Facebook

Ta ce mahaifinsu ya shiga cikin fafutukar Zama Gwamna Kaduna, ne donmin ya inganta zamantakewa da tattalin arzikin jihar da kuma tsaron rayuka da dukiyoyi al-umma.

Ta ce gwamnatin Gwamna Nasir El-Rufai a halin yanzu ta yi wa jihar ayyuka da dama amma akwai bukatar a kara kaimi domin ganin a kara Samar da cigaba a jihar .

Ara’ayinta, Asma’u tace mahaifinta, Sha’aban, shi ne ya fi kowa cancanta da ya gaji El-Rufai, a cikin dukan masu zauracin kujerar.

“Na yi imani yana da dabarar magance matsalar rashin tsaro a jihar da kuma inganta tattalin arzikin kasar,” in ji ta.

Zafafa Labarai