Countdown
Connect with us

Siyasa

2023: Yaron Gwmana Kaduna ya lashe zaben fidda gwani a jam’iyar APC

Published

on

Bello Elrufai, Dan takara Dan Majalisa mai wakilta al’umar Kaduna ta Arewa

Rahotani na bayana Bello Elrufai, yaro ga Gwamna Elrufai na jihar Kaduna, ya lashe zaben fidda gwani na takara kujera dan majalisa mai wakilta al’umar Kaduna ta Arewa.

Kungiyar magoya bayan sa na Bello Elrufai support group (Besg2023), ne suka bayana haka a wani rubutu da Suka walafa a shafin su na Twitter.

Bello, ya Yi kira da a zo a hada kai domin aiki tare nagani an ciyar da kaduna arewa gaba.

Ya kuma yi alkawari cewa zai Samar da abubuwa da dama wanda ba bu a halin yanzu a Kaduna ta arewa.

Ta tabata Bello Elrufai, zai gwabza zabe da Hon. Samaila Sulaiman, wanda yake kan wakilci a halin yanzu, kuma shine yasamu nasara lashe zaben fidda gwani a jam’iyar PDP a zaben 2023.

Zafafa Labarai