Countdown
Connect with us

Tsaro

‘Yan ta’adda sun fitar da hotunan fasinjojin jirgin kasa da Suka sace daga Hanyar Abuja zuwa Kaduna

Published

on

‘Yan ta’addan da suka kai hari kan jirgin Abuja zuwa Kaduna a ranar 28 ga Maris, sun fitar da hotuna da ke nuna wasu fasinjojin da su ka yi garkuwa da su.

Daya daga cikin hotunan wadanda abin ya shafa ya nuna mata da kananan yara, dayan kuma maza zallah.

Idan ba a manta ba ‘yan bindigar sun yi wa jirgin kasan da ke kan hanyarsa ta zuwa Kaduna daga Abuja babban birnin kasar kwanton bauna bayan da suka tayar da bam a hanyar jirgin.

Wasu daga cikin mazan da aka sace a jirgin kasa

Akalla fasinjoji takwas ne suka mutu a lamarin, yayin da aka yi garkuwa da wasu 168 ko kuma aka bayyana bacewarsu.

Kwanaki kadan bayan faruwar lamarin, an sako Manajan Daraktan Bankin Noma (BoA), Alwan Hassan tare da wasu. Hassan, wanda aka gani a wani faifan bidiyo da ‘yan fashin suka fitar, ya ce an sako shi ne bisa dalilai na tausayi.

‘Yan ta’addan dai sun dage cewa za su yi magana da gwamnatin Najeriya ne kawai domin a sasanta a sako mutanen da aka kama.

Zafafa Labarai