Countdown
Connect with us

Tsaro

‘Yan Sanda A Kaduna Sun Kama Wasu Da Ake Zargi Da Safarar Makamai, Sun Kwato Ak 47 Da Kuma Harsashi Masu Rai

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, a ranar Laraba, ta ce jami’anta sun kama wasu mutane biyu da ake zargin suna da hannu wajen aikata laifin safarar
Bindigar AK47 da harsashi Masu rai.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar (PPRO), ASP Muhammad Jalinge, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce a ranar 24 ga watan Afrilu, 2022 da misalin karfe 1330 rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta samu bayanai kan wani da ake zargi da safarar makamai a hanyar kauyen iyatawa na karamar hukumar Giwa, Jihar kaduna.

Ya ce na da nan hukumar ta Samar da jami’ai domin yin sintiri tare da kuma bincika dukan ababan da ke wucewa akan yankin wanda ya sanadin chefke wanda ake zargin.

Ya kara da cewa jami’an ‘yan sandan sun samu nasarar cafke wani Musa lawal mai shekaru 25, da bindiga kirar AK47, dauke da harsashi guda biyu mai girman 7.62 x 39mm.

Ya kuma kara da cewa, a ranar 24 ga watan Afrilun 2022, jami’an tsaron sun kuma sake samun wani kwakkwaran bayani, inda suka kai samame unguwar filin malawa tudun wada da ke cikin birnin Zaria, inda suka kama wani mutum da ake zargi da bindiga kirar AK47 dauke da harsashi 30 mai girman 7.62 x 39mm. Da niyar zai kai wa ‘yan fashi da makami.

ya ce a halin yanzu suna ci gaba da bincike a daidai lokacin da ake ci gaba da kokarin ganin an cafke ‘yan kungiyar domin fuskantar shari’a.

“Wadannan abubuwan ba za su yiwu ba idan ba tare da haɗin kai da kuma saurin bayanai daga membobin al’ummomin ba.”

Ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar Kaduna, CP Yekini Adio Ayoku, yana neman karin hadin kai daga jama’a a fannin musayar bayanai yayin da rundunar ta ke kokarin rage aikata laifuka zuwa ga mafi karanci a jihar.

Zafafa Labarai