Countdown
Connect with us

Tsaro

‘yan bindiga suyi garkuwa da matan wani jami’in soja tare da mutane 6 a kaduna

Published

on

A wani sabon hari, ‘yan bindiga sunyi garkuwa da matar jami’in soja tare da wasu mutane 6 a garin Keke A da B dake yanki sabuwar Kaduna a karamar hukumar Chikun na Jihar Kaduna.

Rahotonin da jaridar Voiceofliberty ta fitar sun bayana cewa, ‘yan bindiga sun kwashe kimani awa guda suna ta’addaci kafin zuwan jami’an tsaro, sun farma garin da misalin karfe 11 daren ranar talata 21 ga watan yuni.

Wani mazauni unguwar ya sheda cewa, maharan sun yi awan gaba da mutane 3 a garin Keke A.

Mutumin wanda malamin firamari ne a daya daga cikin makarantu gari, yace yana zargin ‘yan bindiga sun kawo hari ne gidan qani jami’in soja dake garin Keke A.

” Maharan sun kawo harin ne da karfe 11 dare, Kuma ni Ina tunani sun kawo hari ne wani gida a Keke A. Gidan na wani jam’in soja ne, saidai a lokacin da suka kawo harin sojan baya gida. Maharan sun kutsa cikin gidan inda sukayi garkuwa da mai dakin soja.

” Sun kumayi garkuwa da makwabci soja, inda suka hada da yarsa yar shekara 8 kafin daga bisani suka saki yarinya sabida kururuwa da mahifiyar yarinyar ta dinga yi.

” Daga wanan lokaci ne Suka fara harbe harbe ba kwakwatawa domin razana mutane gudun kada sufito sun tunkare su. Ana cikin hakane, wani dake dawowa a cikin mota ya fada hanun su wanda shine cikon mutum na uku da suka tafi dashi.

” Da safe mugun takalman mutane da yawa Wanda hakan ya tsorata mu, muka fara tunanin ko sunyi a wan gaba da mutane da yawa. Saidai wani wanda ya kubuta ya ce wanan takalma mutane da suka tsere ne.

Wani mazauni a Keke B yace, nadawo gida kenan na shiga wanka na fara jin harbin bindiga.

” a firgice na fita daga bayi, inda naje na kashe dukan wutan gida na. Jin karar harbin su nake a kusa tamkar a cikin gida na. Sai dai na fahimci sunyi garkuwa da wani mutum da matar sa da wasu mata guda biyu. Injishi.

An tuntubi jami’i Mai kula da Hulda da Jama’a na Rudunar ‘Yan Sanda Jihar kaduna, DSP Muhammad Jalinge, inda yace zai tuntubi mu daga baya.

Har yanzu da aka fitar da wanan rahoton bamuji daga gareshi ba.

Zafafa Labarai