Countdown
Connect with us

Tsaro

‘Yan bindiga sunyi garkuwa da dalibai hudu yan Kwalejin Illimi Gidan Waya

Published

on

Kwalejin Illimi, Gidan Waya hoto: SaharaReporters

A qala dalibai hudu ne ‘yan bindiga sukayi garkuwa da su a kwalejin Illimi, Gidan Waya, malakin gwamnatin Jihar Kaduna.

Jaridar SaharaReporters ta rawaito cewa lamarin ya afku ne a daren ranar litini.

A wani sanarwa da Mai magana da yawun bakin kungiyar daliban Jihar kaduna (KADSSU), rashen kwalejin Illimi Gidan waya, Benjamin Fie, ya fitar a ranar Alhamis, yace ” an yi garkuwa da daliban ne a daren ranar litini, a mile 1, Kuma yanzu haka ana bukutar makuden kudade a matsayin kudin fansa kamar ‘yan bindiga suka suka sanar.

” Cikin alhini da bakin ciki, kungiyar dalibai na Yan asalin Jihar Kaduna (KADSSU), rashen kwalejin Illimi, Gidan waya, na sanar da dalibai da jama’a cewa anyi garkuwa da dalibai 4 Yan kwalejin.

” Muna Kira da daukacin daliban kwalejin, mahukuntan, iyaye da Kuma jama’a da su shiga yin adu’oi. Kamar yada sanarwa ta bayana.”

Daliban da lamarin ya shafa sun hada da; Recheal Edwin, Yar aji biyu a tsangayar Biology/Geography, Esther Ishaya, Yar aji biyu a tsangayar Economics/History, Promise Tanimu, Yar aji biyu a tsangayar English/History, sai kuma Beauty Luka, yar aji uku tsangayar CRK.

Sai dai Jami’i Mai Hulda Da Jama’a Na Rudunar ‘Yan Sanda Jihar Kaduna, ASP Mohammad Jalinge, yace bai da rahoton faruwar lamarin, a lokacin da jaridar sahara ta tuntube shi.

Ya ce zai tuntubi Area Kwamanda yanki da abun ya faru, sanan zai sanar da jaridar abubuwa dake akwai.

Zafafa Labarai