Countdown
Connect with us

Tsaro

‘yan bindiga sun yi a wan gaba da ma tafiya tare da raunata wasu a hanyar Abuja zuwa Kaduna

Published

on

A jiya talata rahotonin ke bayana cewa ‘yan bindiga sun sace wasu ma tafiya tare da jikita wasu a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 4 da wasu mintoci, na yamacin ranar talata, a kusa da kauyen Katari, dake kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Wani Ibrahim Muhammad, wanda lamari ya afku a gaban shi ya bayana cewa ” harin ya shafi matafiya dake cikin motoci kirar 406, golf, corola guda biyu, mota mai daukar fasinjoji 18 malaki motocin sifiri na jihar Zamfara, da wasu motocin.

Sai dai maharan su raunata mutane da dama ciki harda kana nan yara, wanda maharan Suka bar su a jefen titi tare da wasu motoci.

Jami’an tsaro da dama ne suka halarci gurin ba yan afkuwan lamari, saidai ba bu wani rahoto dake nuna cewa an kubutar da wani fasinja da aka sace kawo yanzu.

In ba a manta ba a kwana nan ne wasu ‘yan bindiga suka yi musayar wuta da Jami’an tsaro, wanda har yayi sanadiyar mutuwar wani Mai yima kasa hidima akan hanyar ta Abuja Zuwa Kaduna.

Zafafa Labarai