Countdown
Connect with us

Tsaro

‘yan bindiga Sun Saki Sadiq Abdullahi Ango Bayan Shafe Kwana 31 A Hanun Su

Published

on

Sadik Ango Abdullahi

‘yan bindiga da suka kai hari kan jirgin Abuja zuwa Kaduna sun sako Sadiq Abdullahi, wanda da ne a gurin Prof. Ango Abdullahi, shugaban kungiyar dattawan Arewa (NEF).

A ranar Litinin, yan uwan shi su ka tabbatar da cewa an saki Sadiq, a ranar Juma’a bayan ya shafe kwanaki 31 a hannun Yan bindigar.

Yan uwa da abokan arziki sun gano cewa Sadiq, na cikin Wanda akayi garkuwa da su ne a lokacin da Yan bindigar suka saki hotunan mutanen da Suka Kama.

Yan uwan, wanda suka zanta da  jaridar The Nation, ya ce ‘yan bindigar basu San cewa shi dane a gun shugaban NEF a lokacin da a ke tattauna batun sakin sa, ya Kara dacewa sun biya kudin fansa sanan aka sake shi, saidai bai fada nawa Suka biya ba.

Sadiq, ya kasance da daya tilo tsakanin Prof. Abdullahi da marigaya maman taraba, Hajiya Jumai Alhassan. Wanda a halin yanzu yana wani asibiti Ana duba lafiyar sa.

Zafafa Labarai