Countdown
Connect with us

Labarai

‘yan bindiga sun sace mutane a garin Keke B a wani sabon Hari

Published

on

‘yan bindiga sun sace mutane a garin Keke B dake garin Kaduna millennium City na karamar hukumar Chikun.

Wakilin mu ya tataro cewa, ‘yan bindiga sun farmaki garin ne a daren litini.

Rahotonin sun bayana cewa sun shiga garin da misalin karfe 8:30 na dare inda sukai ta harbin kan mai uwa da wabi.

Sun shiga gidajen mutane inda suka Yi garkuwa da mutane Kamar yadda rahotonin ke bayanawa.

Saidai wani bakanike yayi nasara kubuta bayan sun tafi dashi, a na zaton sun tafi da mutane sama da talatin.

Jami’an ‘yan sanda sun shiga garin don bincike yadda lamarin ya faru.

Saidai yayin hada wanan rahoton ba aji daga bakin jami’i Mai kula da hulda da Jama’a na rundunar’yan sanda Jihar Kaduna ba, ASP Muhammad Jalinge.

Zafafa Labarai