Countdown
Connect with us

Tsaro

‘yan bindiga sun sace DPO a Kaduna

Published

on

Wasu ‘yan bindiga a ranar litini sunyi garkuwa da wani DPO ‘yan sanda a yankin Birnin Gwari dake Jihar Kaduna.

A bayanan da Kadunareporters ta tattaro, ‘yan bindiga sun kwashe lokaci suna cin karansu ba babaka a kan titin Birnin Gwari, kafin suyi awan gaba da DPO.

Rohotoni na bayana cewa DPO na kan Hanyar sa ta zuwa Birnin Gwari, inda nan ne sabon gurin aikin sa.

Lamarin ya afku ne a kwana Bola iyakar karamar hukumar Igabi da Kuma Birnin Gwari.

Saidai rahotonin na tabatar da cewa ba iya DPO Yan bindiga sukayi awon gaba dashi ba.

Kawo yanzu babu wani tabaci da aka samu daga rundunar ‘yan sanda Jihar Kaduna akan faruwan lamarin.

Zafafa Labarai