Countdown
Connect with us

Tsaro

‘yan bindiga sun sace dalibai, matafiya tare da Kona motoci a Kaduna

Published

on

A ranar talata wasu ‘yan bindiga suka sace dalibai tare da wasu matafiya a kan baban titi Birnin-Gwari dake karamar hukumar Birnin Gwari a Jihar Kaduna.

Hoto: Kaduna Political Affairs Asali: Facebook

Jaridar Kaduna Political Affairs ta rawaito cewa, akala ‘yan bindiga sun kona matoci takwas na daliban dake hanyan su ta zuwa zana jarabawa makaranta kwalejin lafiya dake Makarfi, wanda zai gudana a Jami’ar Kaduna.

Jami’in hulda da jama’a na kungiyar Birnin Gwari Emirates Progressive Union, Idris Saidu, ne ya bayana hakan a wata sanarwa da yafitar.

Ya kara da cewa, ‘yan bindiga sun kewaye sassa guda uku akan baban titin Birnin Gwari, Wanda ya tursasa direbobi motoci juyawa.

Sai dai wasu matafiya basu iya samu damar tsalake tarkon ‘yan bindiga ba, inda sukayi garkuwa da su.

Sanarwa ta bayana cewa, “Matafiya da dama ne tareda dalibai da zasu je rubuta Jarabawar shiga kwalejin lafiya, Makarfi rashen Jami’ar Kaduna ne ‘yan bindiga sukayi gar kuwa dasu.

Daya daga cikin jami’in mu wanda ya kubata, Abubakar Haruna Babajo, ya bayana cewa akala motoci takwas ‘yan bindiga suka kona bayan sace dukan fasinjoji dake ciki.

Hukumar makaranta ta amince da Sanya sabon ranar jarabawa ga daliban Birnin Gwari tare da taimakon sa bakin Malam Mu’azu Idris.”

A karshe Kunjiyar BEPU, na shawarta masu niyar bin hanya da su dan dakata a halin yanzu ko kuma suyi anfani da wasu hanyoyin domin akwai ‘yan bindiga da dama a gurare uku a kan hanyar.

Zafafa Labarai