Countdown
Connect with us

Da Dumi Dumin Sa

‘Yan Bindiga Sun Nemi Naira Miliyan 3 A Matsayin Kudin Fansa, Bayan Sace DJ A Kaduna

Published

on

Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba, sun yi garkuwa da Dj Ralph Gee, da ke Kaduna.

A cewar abokin mawakin mazaunin Kaduna, Ibrahim Iliya, an yi garkuwa da DJ ne a hanyar sa ta zuwa garin Kaduna daga Kafanchan Kamar yada jaridar kaduna political affairs, ta walafa.

A wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Ibrahim, ya ce, “Abin bakin ciki ne ina sanar da ku cewa dan’uwana kuma abokina DjRalph Gee, babban jami’in DJ na # IBI Live Concert, DjRalph, ‘yan bindiga sun yi garkuwa da shi a ranar 24 ga Afrilu, a hanyarsa ta dawowa daga kanfanchan.”
“‘Yan fashin sun kira ni suna neman kudi #3 miliyan.”

Saidai Ibrahim ya Kara da cewa, masu garkuwa da mutane sun ce a na da mun su da Kira ta wayar Dj, don haka yake Jan hankali abokan dasu guji kiran numbar wayar sa.

Zafafa Labarai