Countdown
Connect with us

Tsaro

‘Yan Bindiga Sun Kashe Shugaban Jam’iyyar APC A Kaduna

Published

on

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari a wasu kauyukan karamar hukumar Kagarko ta jihar Kaduna tare da kashe shugaban jam’iyyar APC na Aribi, Mista Illiya Auta.

An tattaro cewa ‘yan bindigar sun kai farmaki kauyen ne a daren ranar Litinin inda suka kai harin.

An tattaro cewa an yi garkuwa da wasu mutanen kauyen da dama tare da sace daruruwan dabbobi da barayin suka yi.

Ku tuna cewa Kaduna ta kasance cikin tashin hankali sakamakon hare-haren ‘yan bindiga ko ‘yan ta’adda. Na baya-bayan nan shi ne sace wata mata da diyarta da aka yi a ranar Lahadi a karamar hukumar Kachia da ke jihar.

Har zuwa lokacin gabatar da rahoton, babu wani martani a hukumance daga jam’iyyar ko ga ‘yan sanda.

Source: Tribuneonlineng

Zafafa Labarai