Countdown
Connect with us

Tsaro

‘yan bindiga sun kashe mutum 3 tare da raunata 2 a karamar hukumar Kaguru

Published

on

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan mutane gari da masu ibada, sun kashe mutum 3 tare da raunata 2 a Unguwar Fada, Unguwar Turawa da Unguwar Makama dake yankin Rubu na Karamar Hukumar Kaguru.

Jami’an tsaro ne suka tabatar wada Gwamnati Jihar Kaduna faruwa lamarin, Kamar yadda Kwamishina Tsaro Da Harkoki Cikin Gida Samuel Aruwan, ya sanar.

Rahotonin sun bayana cewa, ‘yan bindiga sun kai harin ne a kan babura, inda suka fara daga Unguwar Fada daga na su ka je Unguwar Turawa kafin suka wuce Unguwar Makama dake Rubu.

A kauyen Rubu, sun Kai Hari ne Kan masu ibada a coci Maranathan Baptist Church da Kuma St. Moses Catholic Church.

Kawo yanzu mutane uku sun mutu wanda suka hada da Peter Madaki, Elisha Ezekiel da kuma Shugaban Matasan Rubu Ali Zamani.

Yayin da mutum biyu suka ji ciwuka, saidai rohoton na bayana cewa sun yi garkuwa da mutane da ba a san adadin su ba.

Har ila yau, ‘yan bindiga kuma sun saci kayayeki a shaguna jama’a.

Yayin karban rahoton, Mukadashin Gwamna Jihar Kaduna, Hajiya Hadiza Sabuwa Balarabe, ta nuna matukar damuwa tare dayin Allah wadai da harin, tare da janjanta wa cocika da abun ya shafa.

Balarabe, ta Miki sakon ta’aziyar ta ga iyalen Wanda Suka mutu, tare da yin adu’oi samun lafiya ga wanda suka samu rauni.

Kawo yanzu an baza jami’an tsaro donyin sintiri a yankuna, Kuma Ana cigaba da bincike.

Zafafa Labarai