Countdown
Connect with us

Tsaro

‘yan bindiga sun kashe manoma 2 tare da sace 3 a kaduna

Published

on

Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kashe manoma biyu tare da sace mutum uku a kaduna.

Wasu mahara da ake zargin’yan bindiga sun kashe Manoma biyu a gonarsu dake Iyatawa dake karamar hukumar Igabi, Zaria Jihar Kaduna, Kamar yadda jaridar Dailytrust ta rawaito.

Wani makusanci wanda abun ya shafa ya bayana cewa, Manoman mazauna Kofar Jatau ne dake Zaria, sun tafi gonar su ne domin yin shuka, yayin da ‘yan bindigar suka farmusu wanda hakan yayi sanadiyar mutuwar mutum biyu tare da garkuwa da mutum 3.

DailyTrust a ranar sati, ta gano cewa wanda aka kashe sune Alhaji Mustapha Lawal da Kuma Bello Lawal.

Rohotoni na bayana cewa mahaifin wanda aka kashe Alhaji Lawal Kofar Jatau, ya tsalake harin ‘yan bindiga da kyar a damina da ta wuce a cikin gonar da abin yafaru, saidai ya samu raunuka.

Zafafa Labarai