Countdown
Connect with us

Illimi

Yajin aikin ASUU: Kudaden da ake kashewa kan harkokin siyasa na iya biyan bukatun malamai – Shehu Sani

Published

on

Tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya bayar da shawarar yadda za a kawo karshen yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i, ASUU ke yi.

Sani ya ce kudaden da ake kashewa a harkokin siyasa a Najeriya na iya biyan bukatun ASUU cikin sauki.

ASUU dai ta shiga yajin aikin ne tun watan Fabrairun 2022 saboda gazawar gwamnatin tarayya wajen cimma yarjejeniyar 2019.

Gwamnatin tarayya ta ki amincewa ASUU ta yi amfani da tsarin biyan kudaden da suka samar, wato University Transparency Accountability Solution, UTAS, da dai sauran bukatu.

A yayin yajin aikin da aka tsawaita, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci kungiyar ASUU da ta janye matakin da ta dauka na yajin aiki.

A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu ya fitar, Buhari ya ce “gaskiya ya isa” ajiye daliban Najeriya a gida.

Da yake mayar da martani, Sani ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa: “Idan za ku iya lissafin abin da ake kashewa a siyasa, za ku gane cewa kasar nan za ta iya samun saukin biyan bukatun kudi na ASUU dangane da tsarin jami’o’inmu.”

Zafafa Labarai