Countdown
Connect with us

Illimi

Yajin Aiki: Za a waye gari mu kore ku gabadaya matsawar kuka cigaba da yajin aiki – Elrufai ga ASUU-KASU

Published

on

Gwamna Elrufai na jihar Kaduna ya ce matsawar malaman Jami’ar Kaduna (KASU), ta cigaba da yajin aiki to za awayi gari rana daya an kore su a aiki.

Elrufai ya bayana hakan ne a lokacin da yake gabatar da shiri a gidajen radio dake fadin jihar a jiya laraba.

Da yake amsa tambaaya kan ko shin Malamai Jami’ar Kaduna zasu cigaba da yajin aiki? .

Elrufai yace, ” shugaban jami’ar, na rikon kwarya yace mana sun dawo suna koyarwa wanda bamu tabatar ba.

na sa anbin cika, domin a farko na sa a tsaida albashin su daga baya akace mana su basu yajin aiki nace a cigaba da biyan su, daga baya kuma sai muka ji suna yajin aiki.

Nasa abincika mu tsaida albashin su, Kuma ma wadan da suka karbi albashi kuma basa aikin koyarwa to hakika in aka gama yajin aiki zamu karbi kudaden mu.

Domin dokan Nijeriya, shine in kana yajin aiki to ba maganar biyan albashi.

” Mun Sha fada wa malamai jami’ar Kaduna basu da matsala da gwamnati jihar Kaduna, matsalar ASUU matsala ce da gwamnati tarayya.

Don me yasa malaman jami’ar Kaduna, da ba su da matsala da gwamnati jihar Kaduna zasu cigaba da yajin aiki?.

“In har wanan abun yacigaba zamu iya tashi rana daya mukore su a aiki baki daya, walahi, talahi, billahi zamu salame su duka.

” Aikin su mu buga a jarida mu dauki wasu, domin wanan ba daidai bane karya doka ne, sun tabayin wanan kuma mun gargade su, kuma gashi sun sake yi.

Inajirane insamu rahoto daga Kwamishina Illimi, walahi, talahi zamu Kore su duk ma’aikata KASU dake yajin aiki domin babu wanda zai ce gwamnati jihar Kaduna, ta take hakin sa a KASU.” Inji shi.

Jami’ar Kaduna ita ta kasance a rufe tun daga watan Faburairu duk da a farko ance ba yajin aiki bane, sai daga baya.

Zafafa Labarai