Countdown
Connect with us

Illimi

Yajin Aiki: Muna Kan baka mu ba gudu ba ja dabaya , ASUU-KASU ta fadi matsayarta

Published

on

A karon farko bayan kalaman Gwamna Elrufai kan korar malaman Jami’ar Kaduna (KASU), Kungiyar ta ce fa ita tana yajin aiki Kuma ba gudu ba ja da baya.

Kungiyar malaman ta sanar da hakan ne biyo bayan tattauna wa da tayi da mambobin ta a ranar talata.

Sanarwa mai dauke da sa hanun shugaban kungiyar da sakataren kungiyar rashen jami’ar Kaduna ta bayana cewa.

” biyo bayan tataunawa da ya wakanan a dakin karatu mai daukan mutum 500 wanda ake Kira da (pharm hall), dake jami’ar Kaduna, a ranar 2 ga watan Agusta 2022.

Bayan tattauna wa da kuma yarjejeniya kungiyar ASUU-KASU ta amince da:

  1. Kungiyar zata tattara rahotonin dangane da rashin inganci Jarabawar da yake gudana ta tura wa hukumar bada lasisi jami’oi ta Nijeriya, NUC.
  2. Kungiyar ASUU-KASU bata da hanu gun gudanar da jarabawa dake wakana a jami’ar, saboda yajin aikin da yake gudana wanda tana kan bakan ta babu gudu ba ja dabaya.
  3. Kungiyar ta dauki bayanan karya doka daga mambobin ta dake jami’ar kuma za ta hukunta su daidai da yadda dokar kungiyar ya tanada. “

Jami’ar jihar Kaduna ta dai fara gudanar da jarabawa ta tun daga ranar 1 ga watan Agusta 2022.

Kuma a makon jiya ne dai mai girma gwamna jihar Elrufai ya bayana cewa zai kore dukan malaman jami’ar wanda suke karkashin kungiyar ASUU-KASU matsawar suka cigaba da yajin aiki.

Zafafa Labarai