Countdown
Connect with us

Illimi

Yajin aiki: KASU za ta bude makaranta a ranar 13 ga Yuli, ta nemi fahimtar ASUU

Published

on

Sabon shugaban Jami’ar Kaduna Prof. Abdullahi Ashafa yace Jami’ar zata dawo bakin aiki ranar 13 ga watan Yuli, domin ba wa daliban ajin hudu damar zana jarabawa su takarshe.

Mr. Ashafa ya bayana haka ne a wata hira da yayi da kafani dillanci labarai ta kasa NAN, a ranar juma’a a Kaduna.

Gwamnati Jihar ta shirye bada talafi karatu a kasashen ketare ga dalibai mmasu hazaka.

Yace Dalibai da dama ne zasu ci moriyar talafi bayan kamala karatun su, wanda za a tura kasashen waje domin yin karatu digiri na biyu.

Ashafa ya tabatar da cewa hukumar kulada bada talafi karatu na jihar ta riga ta gama kula yarjejeniyar na tsakanin ta da wasu makarantu biyu a kasashen Africa, inda za’a kai daliban.

Makarantu zasu rufe bada guraben karatu ne a watan satumba, kuma gashi daliban basu rubuta Jarabawar su ta karshe ba sabida yajin aiki da kungiyar Malamai ke gudanar wa a halin yanzu a kasa baki daya.

” A matsayin mu na iyaye muka ga yakamata mu dawo da wuri domin daliban su gudanar da jarabawa su, mu tura ma hukumar talafi sakamokon Jarabawar su domin ta nema musu guraben karatu.” Inji shi.

Yace hukumar makarata ta cima matsaya da manajoji makaranta, domin dawowa 13 ga watan Yuli don cigaba da karatu tare da fara gudanar da jarabawa a ranar 25 ga watan Yuli.

Yayi bayani cewa manjojin Jami’ar wanda suka hada da Dean’s da kuma HODs suke da alhakin tsara gabatar da koyarwa da kuma bincike a Jami’ar.

” Dean’s da HODs sune mayan manajoji Jami’ar wanda masu aiki a kasan su ne ke da alhakin tsara jarabawa, kula da jarabawa tare da bayana sakamakon jarabawa.”

” A wanan Jabar ne za mu gamsar da Gwamnati Jihar da ta biya albashin da ta rike na ma’aikata.”

Ya roki kungiyar Malamai rashen Jami’ar Kaduna (KASU-ASUU), da ta fahimci hukumar makarata a madadin dalibai, sabida kada daliban su rasa damar samun talafin zuwa karatu kasar waje.

Saidai da aka tuntubi Ciyama din kungiyar Malamai rashen Jami’ar Dr. Peter Adamu, yace bashi da masaniyar dawowa makaranta a ranar 13 ga watan Yuli daga hukumar makaratar.

” Nifa yanzu nake jin batun agunku, Ina Mai tabatar muku ba mu daga cikin wanda aka shirya wanan tsarin.” Inji shi.

NAN

Zafafa Labarai