Countdown
Connect with us

Illimi

YAJIN AIKI: Daliban Jami’ar Kaduna na cikin rudani

Published

on

Kofa daga cikin kofofin shiga Jami’ar Kaduna

Dalibai a jami’ar Kaduna na cikin rudani biyo bayan abubuwa dake faruwa tsakanin hukumar makarantar da Kuma kungiyar Malamai ASUU rashen jami’ar, tun bayan sanar da dawo wa makarata da hukumar makarantar ta sanar.

Inza a tuna, tun a watan Faburairu, shekarar nan ne kungiyar Malamai jami’oi a Nijeriya, suka fara yajin aiki, a jami’ar Kaduna a wanan lokaci an sanar dacewa hutun tsakiyar zangon karatu aka tafi bawai yajin aiki da ke gudana ba duk da anyi hutun tun watan disamba 2020 Kamar yadda sabon jadawalin karatun da aka fitar a wanchan lokaci ya nuna.

A wanchan lokacin babu wani rahoto da ya nuna cewa kungiyar Malamai Jami’ar ASUU-KASU, ta fitar domin karyata cewa wanan rahoton da hukumar makaranta ta fitar ba gaskiya bane suna yajin aiki ne.

Dalibai a wanchan lokacin na ta shirye shirye dawowa bakin karatu, inda har an gudanar da zabuka sabin shuwagabanin dalibai, kamar yada jadawalin karatu ya fitar, ama haka lokacin ya wuce shiru ba a dawo bakin karatu ba.

Sai da a ka dau lokaci sai ga sanarwa da ga hukumar makaranta a ranar 26 ga watan Afrilu, inda ta ke cewa dalibai da Malamai su dawo bakin karatu a ranar 9 ga watan Mayu, 2022.

Tun daga wanan sanarwa fa sai aka fara samun martani daga kungiyar Malamai Jami’ar Kaduna ASUU-KASU, inda sukace dalibai suyi watsi da wanan sanarwa domin hukumar makaranta bata da iko yin magana da bakin kungiyar, wanda hakan ne ya kara tabatar wa da dalibai cewa KASU sun shiga yajin aiki.

Daga na fa rahotonin suka fara nuna cewa, dazarar hukumar makarantar ta yi wani yunkuri Kan dawo wa makaranta ga dalibai, sai su kuma kungiyar Malamai su fitar da sanarwa cewa baza su dawo ba Kuma Basu yarda wani dalibi ya dawo ba.

Hakan ya sa daliban makarantar shiga rudani, saidai wasu rahotonin na bayana cewa a yanzu haka wasu dalibai da Malamai sun fara gudanar da karatu musaman daliban dake aji daya.

A baya baya nan dai kungiyar ciyamomi na aji, sukayi taro har suka garzaya ofishin shugaban rikon koryan jami’ar, Prof. Yohana Tella, inda ya tabatar ma da daliban cewa su fada wa dukan abokan karatun su dalibai, da su dawo makaranta domin babu wanda ya ke da ikon bude wa ko rufe makaranta sai hukumar makaranta, kuma ta amince a dawo.

Haka zalika shuwagabanin kungiyar dalibai ma ba abar su a baya ba, domin kuwa suma sun sami ganawa da Prof. Tella, nan ma ya kara tabatar musu da cewa an dawo makaranta, saidai dalibai ne ba su dawo ba kuma ya tabatar musu dacewa kafin juma’a 27 ga watan mayu 2022, za afitar da jadawalin cigaba da karatu.

Hakan yasa suka tun tubi Ciyama din kungiyar ASUU-KASU, a ranar dan ji ta bakin sa, ya kuma sheda musu cewa, su cigaba da fada wa dalibai su dawo makarata domin kuwa zasuyi taro dan duba lamuri inda ya tabatar musu da cewa komai zai daidaita, kamar yadda suka fada a sanarwa da sukayi.

Hakan ya Kara musu karfin gwiwar inda suka je suka samu masu kula da dakunan dalibai akan su bude dakunan domin dalibai zasu dawo, a yamacin ranar ne suka fitar da sanarwa ga dalibai kan abubuwa da Suka tatauna da shugaban makaranta da Kuma Ciyama na Kungiyar Malamai rashen Jami’ar.

Kwatsam a dare ranar sai ga sanarwa daga kungiyar Malamai Jami’ar, cewa basu aminta a dawo ba domin suna ci gaba da yajin aiki har sai an jayen na kasa baki daya, kamar yada karshen tattaunawar su takaya a ranar da sauran Mambobin kungiyar.

Saidai bayan sanarwa ta su an samu anyi karatu ga wasu dalibai musaman yan aji daya.

Mafi yawa daga dalibai dake nesa na cikin tsoro, duba da wata sanarwa daga hukumar makaranta cewa baza a bar dalibi da bai samu Kashi 75 na zuwa aji zana jarabawa ba, ga kuma rahoton da ya riske su na wasu daga cikin dalibai sun fara karatu.

Rahotoni sun tabatar da cewa dalibai musaman na aji daya dai sun fara karatu, Kuma kungiyar ASUU-KASU ba ta hana ba, saidai a sanarwa da ta fitar ne kawai.

Dalibai ‘yan nesa na dai cikin rudani kan wata sanarwa zasu bi suyi aiki da ita, na hukumar makaranta ne ko Kuma na Kungiyar Malamai Rashen Jami’ar?.

Saidai tunda aka fara wanan dambarwa har yanzu, Kwamishina Illimi Jihar bata fitar da sanarwa matsayin Gwamnatin Jihar Kaduna, kan batun dake faruwa a jami’ar ba.

Zafafa Labarai