Countdown
Connect with us

Labarai

YAJIN AIKI: ABUSRC tayi kira ga dalibai jami’ar Ahmadu Bello su fito zanga zanga lumana da NLC ta shirya

Published

on

Kungiyar wakilan dalibai jami’ar Ahmadu Bello (ABUSRC), na kira ga daukacin daliban jami’ar da sufito don goyon bayan zanga-zangar lumana da kunguyar kwadigo ta kasa NLC ta shirya don kawo karshen yajin aiki da malaman jami’oi keyi a fadin Nijeriya.

Kwamured Aliyu Abdulbaqi Bako, Sakataren kungiyar ne yayi kiran a wata sanarwa da yafitar a ranar asabar 23 ga watan Yuli 2022.

Sanarwa ta karanta cewa ” biyo bayan taron mahukunta na kungiyar kwadago ta kasa a ranar 15 ga watan Yuli 2022.

ABUSRC na anfani da wanan damar domin kira ga dalibai jami’ar Ahmadu Bello, su fito domin gudanar da zanga-zanga lumuna da kungiyar kwadago ta shirya gabatar wa.

Kungiyar ta umurta daliban da su zama jakadu jami’ar na gari a yayin gudanar da zanga zanga.”

Malaman Jami’oi dai sun kwashe kimani kwanaki sama da 150 suna gudanar da yajin aiki a fadin Nijeriya, wanda hakan yayi sanadiyar dakatar da harkokin karatu dalibai.

Zanga zangar zai gudana a ranar talata da laraba 26 da 27 ga watan Yuli kamar yadda kungiyar kwadigo ta shirya.

Zafafa Labarai