Countdown
Connect with us

Siyasa

Wike, Ya bayar Da Talafin #200M Ga ‘Yan Gudun Hijira A Kaduna

Published

on

Gwamna Nyesom Wike, ya bayar da talafin naira miliyan dari biyu (#200M), ga Sansanin Yan gudun hijira a Kaduna.

Wike, ya bayar da gudun mawar ne a ranar litini, lokacin da ya ziyarci sakateriyar jam’iyyar PDP, don Neman hadin kai su mara masa baya kan kudirin sa na neman kujerar shugaban kasa a zabe Mai zuwa a inuwar jam’iyar, a kaduna.

” Bai ka ma ta mu kasance masu ra’ayin cin zaben 2023 kadai ba.

“muna bukatar mutane masu jajircewa da cancantar lashe zaben 2023, wannan za mu yi idan kun ba da umarni. A cewar sa”

Wike, ya ka ra da cewa “shawo kan matsalar tsaro da ya adabi kasar Nan, shine wajibi na farko da kowa ce gwamnati ya kamata ta Yi bayan ta dare kan karagar mulki.

Ya kuma ce wata shidan farko na gwamnatinsa shine gani ya dawo da Marta ban kasar nan daga halin da take ciki, inko ba za muyi hakan ba toh babu bukatar muce za mu jagoran ci kasar Baki daya.

Sen. Ahmad Makarfi, tsohon gwamnan Kaduna ya yabi Wike, saboda jajircewarsa
tare da bayyana shi a matsayin dan jam’iyyar da ya tsaya tsayin daka wajen kare muradun talakawa.

makarfi, ya yaba da gudummawar da Wike, ya bayar ga ‘yan gudun hijirar yana mai bayyana hakan a matsayin abin faranta rai.

A nasa jawabin, Mista Flex Hyet, shugaban jam’iyyar na jihar ya ce jam’iyyar a shirya take tsaf domin gabatar da ‘yan takarar da jama’a suka zaba kuma za su wakilci muryar talaka.

Zafafa Labarai