Countdown
Connect with us

Siyasa

Tsohon Shugaban Daliban Jihar kaduna Ya Saye Fom Din Takarar Dan Majalissar dokokin Jiha A Kaduna

Published

on

Comrade Tajudden Kabir Shika, tsohon Shugaban daliban Jihar kaduna a matakin kasa (NAKASS), ya siya fom din takarar kujerar Dan majalisar dokokin jiha don wakiltar al’umar Giwa ta gabas.

Kabir, ya kadamar da aniyar sa na tsayawa ta Karan kujerar dan majalisa ne a ranar 26 ga watan Afrilu, 2022 tare da neman adu’oi tare da goyan baya al’umar karamar hukumar giwa.

Ya kuma garzaya tare da magoya baya, Yan uwa da abokan gaugaurmaye sakateriyar jam’iyyar NNPP mai alamar kayan marmari, inda ya karbi takadar shedan zama dan takara a inuwar jam’iyyar.

Jam’iyyar NNPP dai ita ce jam’iyyar da Eng. Rabiu Musa Kwankwaso, tsohon Gwamna jihar Kano, ya fito neman takarar kujerar shugaban kasa a zabe mai ga batowa.

Zafafa Labarai