Countdown
Connect with us

Tsaro

sojojin Nijeriya sun kara nasara fatatakar’yan bindiga a Kaduna

Published

on

A cigaba da kokarin tabatar da tsaro ya samu a fadin jihar Kaduna, sojojin Nijeriya, sun kara nasara fatatakar ‘yan bindiga a yankin Birnin Gwari, wanda yayi sanadiyar kashe ‘yan ta ada guda biyu.

Kwamishina tsaro da cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan yasanar da hakan a ranar Alhamis a Kaduna.

Yace a cikin rahotonin da suka samu daga sojojin dake aiki tabatar da tsaro, tayi nasara fatatakar ‘yan bindiga a wani samame da ta kai a kan hanyar Birnin Gwari, Doka, Sabon Layi, Kuriga, Mangada da Farin ruwa.

Sojoji sunyi a ran gama da ‘yan bindiga a Farin ruwa, inda sukayi nasara halaka ‘yan bindiga biyu har lahira, tare da tarwatsa sauran ‘yan bindiga.

Gwamnati Kaduna, ta yaba ga namijin kokarin da sojoji sukeyi tare da fatan nasara ga sojojin kan ayyuka dasukeyi.

Zafafa Labarai