Countdown
Connect with us

Labarai

Shugabannin Kiristocin Kudancin Kaduna sun yi Allah-wadai da hare-haren da ake kai wa Firistoci

Published

on

Kungiyar Shugabanin kiristoci na kudancin Kaduna (SKCLA) t a kalubalanci gwamnatin taraya da na jihar Kaduna, da suyi bincike tare da kawo karshen hare-haren da ake kai wa firistoci a fadin Nijeriya.

Bayanin hakan na kunshe ne a wata sanarwa dauke da sa hanu shugaban ta, Apostle Emmanuel Nuhu Kure, a lokacin da yake martani kan labarin kashe Rev. Fr. John Mark Chietnum, daya daga cikin firistoci biyu da akayi garkuwa dasu a Kafanchan.

Apostle Kure, ya bayana karuwa hare hare na garkuwa da firistoci, wanda yace wani lokaci yakan kai ga masu garkuwa dasu na kashe su koda sun karbi kudin fansa.

Ya kuma yi kira ga jami’an tsaro da su jajirce gun gani sun kawo karshen aiyukan ta’adanci baki daya.

Ya kuma bayana mamaci a matsayin mutum wanda ya bada gudumawa matuka a kungiyar tare da bada umarni ga unguwannin kiristoci.

Ya kuma mika ta’aziyar sa ga unguwannin katolika musaman iyalan mamacin tare da adu’a Allah ya tona asirin wanda suka kashe shi, da kuma Allah ya kubutar da duk wanda ke tsare a hanun su.

Zafafa Labarai