Countdown
Connect with us

Siyasa

Shehu Sani ya bayana yada delegates ke tambayar yan takara kudi a lokacin zaben firamari

Published

on

Sanata Shehu Sani yace delegates nada dabarar da suke bi gun tambayar yan takara kudi a wajen zaben fidda-gwani.

Ba Kai tsaye suke cewa suna so dan takara yabasa kudi ba, cewa suke abokin takarar ka ya musu alkawari zai basu abu kaza.

Sanata ya bayana hakan ne a yayin fira da gidan jaridar DW Hausa.

Ya Kara dacewa shi dama ya Sha alwashin ba zai ba kowa ne delegates ko ficika ba, domin basu kudin ba zai kawo gyara ba.

Kuma su suna so ace ankawao gyara a harka zabe tayada delegates zasu Yi zabe bisa chanchanta ba wai dan an basu kudi ba.

Yace, da sun fada maka cewa abokin takarar ka ya musu alkawari zai basu wani abu, to in kaima kanada niyar basu kudi sai kace ka Kara musu abu kaza akan yada ya musu alkawari.

Ya Kuma shawarci duk dan takara da yaba delegates kudi kuma basu zabe shi ba da yabi su har gida ya karba kudin sa domin basu da mutunci.

Sanata Shehu Sani, yace duk da yayi rashin nasara a zaben fidda-gwani 2023, ba zai hana shi tsayawa takara a zabe 2027 mai zuwa ba matsuwar yanada rai da lafiya.

Zafafa Labarai