Countdown
Connect with us

Siyasa

Sanata Uba Sani ya sayi fom ɗin takarar gwamnan jihar Kaduna a APC

Published

on

Sanata Uba Sani lokacin da ya siya fom din takara

Sanata Uba Sani dake wakiltar Kaduna Ta Tsakiya a majalisar dattawa ya sayi fom din tsayawa takarar kujerar gwamnan jihar Kaduna ranar Alhamis.

Sani, da tawagar sa sundira ofishin jam’iyyar APC dake Abuja inda Suleiman Argungu, ya ƙarɓe su.

Bayan ya sayi fom ɗin, sanata Uba yayin ganawa da manema labarai a Abuja, ya bayane cewa,

” Yau dai ya tabbata na siya fom din takarar kujerar gwamnan jihar Kaduna. tare da magoya baya na.

“Babban buri na shine in zama gwamnan jihar Kaduna domin cigaba da kyawawan ayyukan da gwamna mai ci, Nasir El-Rufai ya ke kan aiwatar, Gwamnan da ba a taba yin irinsa ba a jihar, sannan kuma ingina daga nan domin mutanen mu da cigaban jihar mu.

A dayan bangaren kuwa:

‘Yayan Hon. Sani Sha’aban, Sun siya Masa Fom domin tsayawa Takarar kujerar gwamnan Jihar kaduna a Jam’iyar APC

Zafafa Labarai