Countdown
Connect with us

Tsaro

Sajoji sunyu nasara halaka ‘yan bindiga biyu akan hanyar Zaria-Kaduna

Published

on

Dakarun sojin kasa ta Nijeriya, sunyi nasarar halaka ‘yan bindiga biyu a garin Fondisho dake kantitin Zaria-Kaduna, na karamar hukumar Igabi.

Kwamishina tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, ya bayana haka yau laraba a Kaduna, a wata sanarwa da yafitar.

A rohotonin tsaro da gwamnati Kaduna ta samu, sojoji sun yi hanzari halarta yakin da lamarin ya afku biyo bayan samu rahotonin siri da sukayi. Inji sanarwa.

Sojojin sun shirya dabaru inda daga bisani sukayi musayar wuta da ‘yan bindiga, wanda yayi Sana diyar halaka ‘yan bindiga biyu, wasu kuma sun gudu da raunuka harbi a jikin su.

Gwamnati Kaduna tayi matukar jinjina ga jami’an soji tare da jami’an tsaron, ta kuma karfafe su da su kara jajircewa wajen tabatar da tsaro a fadin kasar.

Gwamnati ta Kara da kira mazauna yakin da su kai rahoton duk wani da basu gamsu dashi ba wanda yake bukatar kulawar asibita, sakamokon da dama daga ‘yan bindiga sun gudu da raunuka harbi.

Zafafa Labarai