Countdown
Connect with us

Tsaro

Rundunar Yan Sandan Jihar Kaduna Ta Baza Dakaru Na Musamman 10,000 Domin Tabatar Da Tsaro Yayin Bukukuwan Sallah

Published

on

Hoto: YASUYOSHI CHIBA/AFP Asali: Getty Images

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna a ranar Asabar din da ta gabata, ta ce za ta baza jami’anta 10,000 a fadin jihar domin dakile duk wata barazanar da zai kawo sanadin karya doka da oda a lokutan bukukuwan Sallah.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan (PPRO), ASP Mohammed Jalinge ya fitar.

Jalinge ya ce an samu tura dakarun ne daga cikin fanni ka da dama na rudunar domin tabbatar da gudanar da bukukuwan Sallah lafiya.

Ya kara da cewa, za a baza jami’an 10,000 wuraren sallah, kasuwanni, manyan tituna da sauran wuraren taruwar jama’a.

Ya ce, kwamishinan ‘yan sandan jihar Kaduna, CP Yekini A. Ayoku, ya na Mai tabbatar wa jama’a cewa tsaron lafiyarsu da kare su, na da matukar muhimmanci ga rundunar.

ya kuma jawo hankalin iyaye
domin su fadakar da ‘ya’yansu da ka da su shiga cikin masu karya doka da oda, domin duk wanda aka Kama da laifin karya doka da oda zai fuskanci hukunchi kamar yadda doka ta tanada.

Zafafa Labarai