Countdown
Connect with us

Tsaro

Rundunar ‘Yan Sanda Sun Tantance Masu Neman Aiki 3,583 A Kaduna

Published

on

Rundunar ‘yan sanda a jihar Kaduna ta ce ta tantance mutane 3,583 da suka zana jarabawar CBT wa to Computer Based Test a Kaduna, kan daukar aikin ‘yan sanda a Fadin kasar.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Mohammed Jalige, ya shaida wa manema labarai a Kaduna cewa, yunkurin daukar ‘yan sanda 10,000 ya kara kaimi, inda ya kara da cewa an tantance mutane 3,583 cikin nasara a tsakanin ranakun 20 zuwa 21 ga watan Afrilu, 2022 a jihar.

A cewarsa, an zabo masu neman ne daga wadanda suka halarci aikin tantancewa na karshe da suka yi a jihar sannan suka zana jarabawar Computer Based Test (CBT) a wurare biyu a cikin birnin Kaduna.

Ya ce masu neman takarar da suka zauna CBT su jira sakamakon sakamakon da za a bayyana nan ba da jimawa ba.

Zafafa Labarai