Countdown
Connect with us

Labarai

Rufe iyakokin Najeriya bai amfanar da komai ba; Kamata Yayi A Bada Hakuri Yayin Sake Bude Su – Shehu Sani

Published

on

Tsohon sanata kaduna ta tsakiya kuma Dan takarar kujera Gwamna jihar Kaduna Comrade Shehu Sani, ya bayyana cewa Rufe iyyakokin Nijeriya, bai amfanar da komai ba, kamata yayi Gwamnati ta ba da hakuri yayin sanar da bude iyyakokin.

Sani, ya baya na hakan ne a shafin da na tuwitta inda ya walafa cewa “
Rufe iyakokin Najeriya bai amfanar da komai ba; Kamata Yayi A Bada Hakuri Yayin Sake Bude Su.”

Gwamnatin tarayya ta bayar da umarnin sake bude wasu iyakokin kasa guda hudu da aka rufe a watan Agustan 2019.

A wata sanarwar da hukumar kwastam ta Najeriya (NCS) ta fitar a ranar Juma’a mai dauke da sa hannun mataimakin kwanturola-janar na hukumar E.I Edorhe, gwamnatin tarayya ta umurci hukumar ta kwastam ta bude iyyakokin Idiroko, jihar Ogun; Jibiya, Katsina State; Kamba, Jihar Kebbi da Ikon, Jihar Kuros Riba.

Zafafa Labarai