Countdown
Connect with us

Rahotoni

RESCUEKSCOE sun fara tattauna batun shawo kan matsalar halin da kwalejin illimi Gidan Waya ke ciki

Published

on

Wasu dalibai masu kishi kwalejin illimi Gidan Waya, kar kashin RESCUEKSCOE sun fara tattaunawa Kan batun shawo matsalar da kwalejin ke fuskanta na rashin kyaukyauwar muhalin karatu.

Daliban dai sun gudanar da tatunawar su na farko a kafar zoom, a ranar laraba da misalin karfe 7:30 na dare.

In za a tuna a makon da yagabata ne shugaban kungiyar dalibai Jihar Kaduna reshan kwalejin, ya yi kira ga Gwamnati Jihar Kaduna, kungiyoyi masu zaman kansu, tsofin dalibai cewar akwai bukatar su zo su kawo musu dauki Kan halin da muhali kwalejin ke ciki.

Tataunawa yasa mu halacin wasu daga cikin dalibai, tsofin daliban kwalejin, shuganin dalibai, wakili daga kungiyar Civil Society, da yan jarida.

A yayin jawabi, Shedrack Danladi, wanda shine ya jagoranta gudanar da taron yace, “wanan taro ne da samarda shawarwari Kan shawo kan matsalar rashin kyaukyauwar muhalin kwalejin mu da labari sa ya karade Gidan jaridu da kafar soshiyal midiya.

Taron mu a nan bayana nufin mu kungiya bane da za muyi fito na fito ko cin zarafin Gwamnati ko hukumar makarata ko Kuma wani.

mun taru ne ayau don mu tattauna halin da makarantar mu ke ciki, domin samo mafita akan matsalar rashin kyaukyauwar gine gine.

Ana sa jawabin shugaban kungiyar dalibai Jihar Kaduna reshan kwalejin, Danladi Louis Ninyio yace, ” halin da yaga makaranta na ciki ne na rashin kyaukyauwar muhalin karatu, ya sanya shi yin Kira ga masu ruwa da tsaki don gani sukawo musu dauke.”

Wasu da suka tofa albarkacin bakin su a taron ga abin da suke cewa:

Salmanu Muhammad, tsohon dalibi ne daya Kamala karatu a Kwalejin a Shekara 2005 yace, ” yakamata ace makaranta na cigaba ne ba cibaya ba. Akwai bukatar kafa kungiyar tsofin dalibai (ALUMNI) domin suma su ba da gudunmawa gun gani makaranta ta cigaba.”

Comrade Godiya Adamu, a yayin jawabin ta tace, ” matsalar dakin kwana dalibai ne yafi tayar Mata da hankali, domin ita ta kasan ce ta nason zaman dakin dalibai ama rashin kyauwan sa ya tilasta mata kama daki a waje makaranta.”

A lokacin da nagama NCE a dakin kwana makarata na zauna, ama yanzu rashin kyaukyauwar muhalin yasa dole a wajen makaranta na Kama daki, wanda hakan ya saba ma tsarin na ama ba yadda na iya. Injita.

Wani dalibi shima ya Yi kira ne dacewa, akwai bukatar a bada mahimanci gun gani an gyara dakin kwana dalibai domin dalibai na Shan wahala ga Kuma tsadar haya da suke fama dashi.

Zafafa Labarai