Countdown
Connect with us

Siyasa

Rashin Tsaro Ya Maida Jihar Kaduna Tamkar Shekara 50 Da Suka Wuce – Hon. Ashiru Kudan

Published

on

Hon. Isah Ashiru Kudan hoto: ATM movement Asali: Facebook

Dan takara kujerar gwamna jihar kaduna, a karkashin jam’iyar PDP Hon. Isa Ashiru Kudan, ya bayana cewa rashin tsaro da Jihar kaduna ke fuskanta ya maida Jihar baya, kamar shekara hamsin da suka wuce.

Ashiru, ya zargi jam’iyar APC da haifar da rashin hadin ka al’umar jihar, inda ya ce da zarar ya zama gwamna jihar zai kawo karshen matsalar rashin tsaro da take adaban jihar tare da Samar da hadin kai tsakanin al’umar jihar baki daya.

Ya bayana haka ne a lokacin da yake kadamar da cibiyar yakin nemar zaben sa, ya kara da cewa ba zai bar wata gibi da zai kawo cigaba a Jihar matsawar ya dare madafun iko.

“Matsalar tsaro a jihar kaduna shi ya haifar ma da Jihar koma baya tamkar shekaru 50 da suka shude, ba za ayi maganar cigaba ba matsawar akwai rashin tsaro da rashin hadin kai al’uma a cikin jiha. “

Ba na fito takara bane domin Ina so na zama gwamna kawai, domin ko aiki ne mai wahala dole akwai ranar da za ka tsaya a gaban Allah kayi masa bayani. Ni na fito ne sabida bazan iya jure gani Jihar a yanayin da take ciki sabida nasan akwai rawar da zan iya takawa domin Kawo karshen matsalolin da Jihar ke fuskanta. A cewar Ashiru.”

Zafafa Labarai