Countdown
Connect with us

Labarai

Ranar Rigakafi: Kaduna ta samu lambar yabo matsayin jiha da ta fiko kowa cikin jihohi Arewa maso Yamma

Published

on

An karama jihar Kaduna da lambar yabo a matsayin jiha da ta zarce dukan nin jihohi shiyar Arewa maso Yamma gun gudanar da alurar rigakafi.

Jihar ta samu lambar yabbon ne a yayin bikin makon rigakafi Afrika na shekarar 2022.

Mukaddashin Gwamna, Dakta Hadiza Sabuwa Balarabe ta karbi lambar yabon ne a wajen bikin bayar da lambar yabo ta allurar rigakafi na shekarar 2022 da aka gudanar a dakin taro na Ladi Hall, Sheraton Hotels and Towers, Abuja ranar Juma’a 26 ga watan Agusta 2022.

Hukumar Kula da Lafiya a matakin farko ta kasa ce ta shirya taron domin bikin Makon rigakafin Afirka na 2022 da kuma cika shekaru uku da Najeriya da samun takardar shaidar saukin cutar shan inna.

Zafafa Labarai