Countdown
Connect with us

Labarai

RAMADAN: Sheikh Gumi Ya Ziyarci Manyan Asobitoci A Karamar Hukumar Kaduna Ta Kadu Da Arewa, Inda Ya Rabawa Majinyata Kudi

Published

on

Dr. Gumi yayin ziyara asibiti Hoto: Dr. Gumi media team Asali: Facebook

Bayan Kamala tafsiri watan Ramadan na shekarar 2022, Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi, ya ziyarci manyan asibitoci guda biyu a karamar hukumar kaduna ta kudu da kaduna ta arewa inda ya rabawa ma jinyata kudi.

A safiyar ranar sati 30 ga watan afrilu, 2022 Sheikh Gumi, ya kai ziyara asibiti Gwamna Awan dake karamar hukumar kaduna ta kudu da kuma asibiti Barau Dikko Wanda ke karamar hukumar kaduna ta arewa.

Ziyarar ta sanya Sheikh Gumi, ya Kara fahimtar yana yi kunci da wahala da majinyata ke ciki na rashin kudi da samun masu da duk da yawan masu arzikin da muke dasu tare da tabar barewar harkar kiwon lafiya.

A yayin ziyarar, Sheikh Gumi ya bayar da kyautar kudi ga marasa lafiya tare da yin kira ga masu hannu da shuni a cikin al’umma da su taimaka wa marasa galihu a cikin al’umma, musamman ma wadanda ke fama da lalurar da ba za su iya daukar nauyin samun kulawar lafiya ba.

Lokacin ziyara asibiti Hoto: Dr. Gumi media team Asali: Facebook

Malamin ya bayyana kaduwarsa da wannan lamari mai cike da bakin ciki da ya gani, inda ya ce ya kasa yarda cewa a kasar da ke da hamshakan attajirai, galibinsu, wadanda ya ce suna tara dukiya ne ta hanyar samun tagomashi daga gwamnati ko kuma ta hanyar cin hanci da rashawa ta hanyar nade-nade ko Kwangiloli, har yanzu mutane suna cikin wahala da kunci.

Ya kuma bukaci gwamnatoci a dukkan matakai da su samar da karin kayan aiki a asibitocin gwamnati, da sanya likitoci su rika duba marasa lafiyan tare da samar da hanyoyin bada talafin biyan kudaden don duba marasa lafiya, musamman wadanda ke cikin mawuyacin hali.

Zafafa Labarai