Countdown
Connect with us

Labarai

Ramadan: Rachael Averik Ta Bada Tallafin Abinci Ga Musulmai

Published

on

Shugaban mata na jam’iyyar APC na shiyya ta 3 a Kaduna, Honarabul Rachael Averik, ta bayar da tallafin abinci ga wata makarantar Islamiyya da ke Barnawa Kaduna.

Shugabar matan da ta ga akwai bukatar a mayar wa al’umma, ta ce hanyarta ce ta bayar da gudunmawa domin dakile matsanan cin hali da ke faruwa a cikin watan Ramadan.

Averik ta bayyana cewa abubuwa sun kasance masu wahala ga mutane da yawa kuma buƙatar bayarwa don tafiya cikin al’umma ya zama dole.

Dalibai sai murna sukeyi yayin da ta ke cin abinci tana wasa ta re dasu.

Da yake mayar da martani, daya daga cikin malaman addinin Islama na makarantar ya yaba mata tare da addu’ar Allah ya kare ta ya kuma daukaka ta.

“A ce budurwa kamar ki ta yi tunani haka, yana nufin har yanzu akwai mutanen kirki a kasar,” in ji shi.

Credit: kaduna political Affairs

Zafafa Labarai