Countdown
Connect with us

Labarai

NUT ta caccaki gwamnatin Kaduna, ta ki amincewa da korar malamai 2,357

Published

on

Gwamnati Jihar Kaduna na fuskanta barazanar yajin aiki daga kungiyoyi ma’aikata biyo bayan korar malaman makaranta firamari sama da dubu biyu da kungiyar illimi na baidaya jihar (KADSUBEB) tayi sabida faduwar Jarabawar chanchanta.

Kungiyar Malamai Nijeriya (NUT) ta sha alwashin tsunduma yajin aiki a kasa baki daya matsawar Gwamnati Jihar Kaduna ba ta janye kudirin ta na korar malamai da tayi ba tare da shugaban Kunjiyar NUT na kasa, Audu Amba.

Kungiyar NUT ta tabatar da matsayin ta ne bayan taron masu ruwa da tsaki da tayi a gidan Malamai, dake Lugbe a baban birnin taraya Abuja.

In za a tuna kungiyar Yan kwadigo ta kasa ta gudanar da yaji aiki na tsawon sati guda a Jihar Kaduna a ranar 18 ga watan mayu 2021.

Kan nuna rashin amincewa da yada Gwamnati Jihar ba ta ke afani sha’anin ma’aikata, tare da dakatar da abubuwan jindadi mutane da suka hada da wutan nepa da sauran su.

A kwana na uku ne dai a ka janye yajin aiki biyo bayan Kiran zaman sulhu da minista kwadigo yayi tsakanin Gwamnati Jihar Kaduna da kungiyar Yan kwadigo.

A ranar 19 ga watan yuni 2022 hukumar illimi baidaya jihar Kaduna ta sanar da korar Malamai firamari 2,357 bisa faduwa jarabawa chanchanta, inji Mai magana da yawun bakin hukumar, Hauwa Muhammad.

Yayin ganawa da manaima labarai, mataimaki shugaban kungiyar NUT ta kasa, Dr. Kelvin Nwankwo, yace shugaban kungiyar Bai fadi wata jarabawa gwaji ba, kuma yana nan daram a matsayin shugaban kungiyar.

Zafafa Labarai