Countdown
Connect with us

Illimi

Nuhu Bamali Politeknik tayi martani Kan wani video dake yawo a kafafen sada zumunci dauke da dalibai a cikin aji da rufin shi ya lalace

Published

on

Makarantar Kimiya da fasaha ta Nuhu Bamali Politeknik, Zaria, tayi martani Kan wani video dake yawo a kafafen sada zumunci, wanda ya nuna wasu dalibai na gudanar da jarabawa a ajin da rufin shi ya lalace.

A wani sanarwa da yafito dauke da sa hanu jami’i Mai kula da bayanai na makarantar, Abdullahi Ibrahim Shehu, inda yace ana so ne a bata sunan makarantar a gun Jama’a.

” Biyo bayan wani video da yake yaduwa akafafen sada zumunci, wanda yake nuna wasu dalibai na zana jarabawa a cikin aji wanda rufin sa ya lalace a daya daga cikin makarantu Nuhu Bamali Politeknik, Anex, wanda ke Kan titin gaskiya, bakomai bane ila aikin masu son Bata sunan makarantar da kuma Gwamnatin Jihar Kaduna.

Muna sanar da cewa makarantar na da isasun ajujuwa da ake bukata, kuma tun da rufin ya lalace a shekarar da ta gabata aka dai na anfani da ajin.

Bincike yanuna cewa sabida Samar da tsaro ne a yayin jarabawa zango na biyu dake kan gudana, yasa wasu Masu kula da jarabawa suka ce dalibai su shiga cikin ajin, wanda ake ma lakabi da multipurpose hall.

Tun a ranar 18 ga watan Mayu, 2022 aka fitar da dukan kudin da zai isa ayi aikin gyara ajin, tare da taimakon wani dan siyasa da kuma wani tsohon dalibi makaratan.”

Hoton cikin ajin daga cikin video Hoto: Hashim Suleiman Asali: Facebook

Bincike da jaridar kadunareporters tayi tagano cewa, video dai an sake shi ne kwana uku da suka wuce a shafin Facebook din wani Muhammad Hashim Suleiman.

Suleiman a tare da video ya bayana cewa ” wanan yau kenan, Makarantar Kimiya da fasaha ta Nuhu Bamali Politeknik, (School of Management), Zaria-Nigeria. Wadanan dalibai ne dake rubuta jarabawa a daya daga cikin makarantu malakin Gwamnatin Jihar Kaduna. Har sai yaushe zamu farka? Ko dan yaran masu hanu da shuni basu karatu a irin wadanan makarantu ne? Ku dubi hatsari dake tatare da dalibai a irin yanayin da suke. Wanan Jihar Kaduna ne inda Gwamnatin ke ikirarin inganta harkar illimi? In ka san cewar wanan Politeknic daya ditilo malakin Gwamnatin Jihar, a yanayi na rashin ingatatun gine gine, Ina makomar sauran gine gine makarantu malakin Gwamnatin Jihar?.

Hoton aji daga video Hoto: Hashim Sulaiman Asali: Facebook

Kadunareporters ta Kara da tuntubar wasu dalibai dan jin taba kinsu ama daliban sunce ba zasu iya cewa komai ba.

Saidai kadunareporters tayi kokarin jin ta bakin Shugaban daliban makaranta, ama ba ta same shi ba.

Zafafa Labarai