Countdown
Connect with us

Siyasa

Nayi farin ciki matuqa daukar Hadiza matsayin matemakiyar Uba Sani – Datijjo

Published

on

Dan takarar kujera Sanata kaduna ta tsakiya a inuwar jam’iyyar APC, Muhammad Abdullahi Datijjo ya bayana farin ciki daukar Dr. Hadiza a matsayin mataimakiyar Ina Sani a Zaben 2023.

“Ni  na fi kowa farin ciki da murnar ɗaukar Hadiza Balarabe mataimakiyar gwamna da ɗan takarar gwamna Uba Sani yayi. Yin hakan nuni ne cewa ana tafiya tare kuma tare za akai ga ci da nasara. “

Hadiza tana da kwarewa da sanin yadda ayyuka suke tafiya a jihar Kaduna wanda hakan zai sa a samu tafiya da ɗorewa mikakkiya idan gwamnati sabuwa ta dare karagar mulki.

Bayan haka Dattijo ya yabawa wa ƴan jam’iyyar da shugabannin ta da suka yi zurfin tunani wajen zaɓin ta, domin ta yi wa Uba Sani mataimakiyar gwamna.

Datijo shine yayi nasara lashe zaben firamari na kujerar Sanata kaduna ta tsakiya.

Wanda a farko shima yafito neman kujerar gwamna jihar ne, kafin daga bisani Gwamna Elrufai ya bashi shawaran ya janye wa Uba Sani, shikuma ya nema kujera Sanata Kaduna ta tsakiya.

Zafafa Labarai