Countdown
Connect with us

Da Dumi Dumin Sa

Nan Ba Da Jimawa Ba, Jirgin Kasa Abuja Zuwa Kaduna Zai Cigaba Da Zirga Zirga – NRC

Published

on

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen kasa ta Najeriya, NRC, a ranar Alhamis, ta ce ta samu nasarar kammala aikin da aka lalata na layin dogo daga Abuja zuwa Kaduna, biyo bayan harin da ‘yan ta’adda suka kai a ranar 28 ga watan Maris wanda ya hana zirga-zirga a kan hanyar.

Idan dai za a iya tunawa, harin ya yi sanadin mutuwar mutane tara tare da yin awon gaba da mutane da dama, ciki har da wata tsohuwa, wata mata mai shayarwa, da dai sauransu.

A cewar wata sanarwa da aka rabawa manema labarai, NRC ta ce an cimma Kamala gyaran hanyar shiga tsakanin garuruwan biyu, ko da yake ta kasa bayar da cikakken bayani kan mutane 141 da har yanzu ke hannun wadanda suka sace su.

Niyi Alli wanda ya sanya hannu a madadin Manajan Daraktan Kamfanin, Fidet Okhiria, sanarwar ta ce: “An samu nasarar hada layin jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna (AKTS). Wannan yana nuna cewa an kamala shimfiɗa dukan abubuwa da ake bukata wanda ya lalace sanadiyar bom din da aka dasa a layin dogo. Yanzu aikin titin dogon hanyar shiga tsakanin Abuja da Kaduna ya kamalu.

“Musu gyara hanyar na cigaba da ganin sun tabatar da cewa sun Kuma la dukan wani gyare gyare, inda suke ci gaba da daure daure da walda guraren dake da bukata.

“Loco 2502, jirgin da hatsarin ya rutsa da shi (duk da cewa bai lalace ba) ta makale a karshen Rigasa saboda rashin hanyar da za ta bi, a yanzu haka tana gurun gyara domin a duba lafiyar jirgin tare da inganta shi.

“Kamar yadda muka bayyana a cikin jawabin mu a baya, nan ba da jimawa ba za a ci gaba da zirga-zirgar jiragen kasa daga Abuja zuwa Kaduna tare da samar da karin matakan tsaro.

Hukumar ta NRC ta ci gaba da cewa, “Za a bukaci fasinjoji su ba da numbobin rajistar shedar dan kasar su(NIN), don tantancewa kafin su sayi tikitin jirgin kasa. Wanda hakan zai kara inganta hanyar samun bayanan fasinja da aminci a cikin jirgin.

“Kamfanin ya himmatu wajen kare lafiyar dukkan fasinjojinmu da ma’aikatanmu da ke cikin jirgin Ak9 marassa lafiya. Za mu ci gaba da hada kai da jami’an tsaro domin ganin an kubutar da duk wadanda ake tsare da su ba tare da sun ji rauni ba kuma domin sake haduwa da iyalansu nan ba da jimawa ba.

“A cikin bin umarnin shugaban kasa, muna karfafa duk wanda har yanzu yana neman masoyi, ko dan uwansa da ya tuntuɓar lambobi Kamar haka:
Mrs. Lola akan 08023310145 da Mr. Mahmood akan 07038356015″

Zafafa Labarai