Countdown
Connect with us

Da Dumi Dumin Sa

Mutum daya ya mutu yayin da ‘yan bindiga sukayi garkuwa da mutune a garin Kurmin Sata

Published

on

A qalla anyi garkuwa da mutum ashirin a wani harin ‘yan bindiga da ya afku a daren ranar juma’a, a unguwar Kurmin Sata, kilomitoci kadan kusa da sabuwar kaduna (millennium city), a karamar hukumar chikun, na jihar Kaduna. Inda rahotonin ke bayana cewa mutum daya ya rasa ransa.

Yayin zantawa da mane ma labarai, daya daga cikin shugaban Yan sakai (JTF), mazaunin yankin da ya bukaci a sakaya sunan sa ya bayana cewa, da misalin karfe 12 da minti 6 na dare ranar juma’a ne ‘yan bindigar Suka afkawa garin Kurmin Sata.

” Cikin mutum ashirin da suka yi garkuwa dasu, hudu da suka hada da mata biyu da maza hudu, sun ku bata a yayin harin.

” Cikin mutanen da lamarin ya hada dasu akwai sarkin yanki, masu rike da saurata, mata da yara. Yayin da suke harbin Kan mai uwa da wabi ne batachan harsashin ya samu wani mutum dake cikin gidan sa wanda yayi sanadiyar mutuwar sa.

Ya Kara dacewa ‘yan sanda dake sabon birnin Kaduna (millennium City), sun zo garin da safe.

Zafafa Labarai