Countdown
Connect with us

Tsaro

Mutum daya ya mutu, da dama sun jikkata sakamakon arangamar ‘yan sanda da ‘yan Shi’a a Kaduna

Published

on

Mabiya shi’a

Akalla mutane tara ne rahotanni suka ce sun samu raunuka bayan da ‘yan kungiyar (IMN), wacce aka fi sani da Shi’a, suka yi artabu da jami’an ‘yan sanda a jihar Kaduna.

An tattaro cewa rikicin ya fara ne a lokacin da ‘yan Shi’a suka mamaye manyan titunan acikin birnin Jihar a ranar Juma’a domin gudanar da jerin gwano domin tunawa da ranar Qudus ta kowace shekara.

An saba gudanar da taron ne da jerin gwano a ranar Juma’ar karshe ta watan Ramadan don nuna adawa da mamayar da Isra’ila ke yi wa Falasdinu.

Rahotanni sun bayyana cewa jami’an tsaro da aka girke a manyan titunan Kaduna da Zariya sun yi kokarin tarwatsa gungun masu zanga-zangar amma lamarin ya rikide zuwa tashin hankali.

Wani ganau ya shaida wa manema labarai cewa ‘yan sandan da aka girke sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye da kuma harsasai masu rai a kan masu zanga-zangar yayin da wasu ‘yan Shi’a kuma suka kona motoci da dama a Zariya.

Amir na IMN a Kaduna, Aliyu Umar, wanda ya zanta da manema labarai, ya kara da cewa, ranar Kudus ta kowace shekara, taron duniya ne, kuma ana tunawa da shi hatta a kasashen yammacin duniya. Sai dai ya ce yana mamakin dalilin da ya sa jami’an tsaro ke yawan afkawa kungiyar a duk lokacin da suke bikin ranar.

A nasa ruwayar Umar ya ce muzaharar ta kasance cikin lumana kuma an yi kokarin kaucewa ’yan sandan da tuni aka ajiye su a wani wuri mai ma’ana don tarewa. “Amma sun bi ta baya suka yi amfani da barkonon tsohuwa da harsasai masu rai a kan mambobinmu. An harbe mutum daya har lahira; yanzu mun gudanar da Sallar Janazah, yayin da mutum tara suka samu raunukan dalilin harsashi da yansanda Suka harba ,” inji shi.

Amir ya kuma ce rundunar ‘yan sandan ta kama wasu ‘yan kungiyar kusan takwas tare da musanta zargin cewa an kona ofishin ‘yan sanda da kuma cewa ‘yan Shi’a sun kona motoci.

Har yanzu dai rundunar ‘yan sandan jihar ba ta mayar da martani kan abin da ya faru da ‘yan Shi’ar ba.

Zafafa Labarai