Countdown
Connect with us

Siyasa

Mutum biyu da suka zabe ni sun chanchanchi godiyata da na san su – Shehu Sani.

Published

on

  • Mutane biyu da suka zabeni sun chanchanchi na gode musu domin sun zabeni me bisa ga chanchanta ba wai dan na ba su ko sisi ba.
  • Shehu Sani yataya Hon. Ashiru Kudan murnan lashe zaben fidda gwani na Jam’iyar PDP.
Comrade Shehu Sani.

Tsohon Sanata Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani, kuma Dan takara kujera Gwamna Jihar Kaduna a jam’iyar PDP, da yasha kayi a zaben fidda gwani da a kayi jiya, inda yasa mu kuri’u guda biyu kachal, ya bayana cewa mutum biyu da suka zabe shi sun chanchanchi yayi musu godiya.

Ya bayana hakan ne a wani rubutu da ya walafa shafin sa na Twitter, jim kadan bayan an fitar da sakamokon zaben.

Yace “an Kamala zaben fidda gwani ‘yan takara kujera Gwamna na jam’iyar PDP a Kaduna. Nayi rashin nasara yayin da Hon. Isah Ashiru Kudan, ya lashe zaben. Ina matukar Taya sa murna. Delegates biyu ne kachal suka zabe ni ba tare da na ba su ko ficika ba. Saidai, ban san suba da nagode musu bisa wanan kuri’u da suka bani.”

Tun kafin zaben dai, Sanata Sani, ya bayana cewa ba zai bawa kowa ni delegates ko ficika ba domin ya zabe shi.

Zafafa Labarai