Countdown
Connect with us

Labarai

Mune muka tsaya Saida aka mayar da malaman Jami’ar Kaduna 3 da a ka kora aiki – Shugaban ASUU

Published

on

Emmanuel Osodeke, shugaban Kungiyar Malamai Jami’oi a Nijeriya, ya bayana cewa kungiyar ASUU ne suka yi tsayin daka har saida a kamayar da Malaman Jami’ar Kaduna (KASU), aiki bayan da Gwamna Elrufai ya kore su.

Yafadi hakan ne a ranar sati, a wani shiri na musaman a gidan radio Berekete Family dake Abuja, domin samo bakin zare yajin aiki kungiyar Malamai a Nijeriya.

Osodeke yayin amsa tamabaya matsayar kungiyar ASUU Kan hukunta Malamai da suka saba qa’idar aiki.

Yace, ” kungiyar bata goyon bayan wani malami matsawar ya saba qa’idojin aiki, Kuma yace kungiyar baza ta lamunta korar Malamai, ba bisa bin tsarin doka ba.”

Yayin bada misali, ya bayana cewa kungiyar ASUU ce tayi ruwa tayi tsaki har saida a kadawo da Malamai 3 na Jami’ar Kaduna (KASU) wanda Gwamna Elrufai, ya kora kawai don sun shiga zanga-zanga da ya guda na a jihar tare da kungiyar Yan kwadago.

Zafafa Labarai