Countdown
Connect with us

Da Dumi Dumin Sa

Mita wuta kyauta ne, Kaduna Electric ta magantu

Published

on

Mita wuta kyauta ne inji hukumar wutar lantarki Jihar Kaduna..

Kamfani rarraba wuta lantarki na Kaduna Electric, me alhakin raba wutar lantarki a fadin jihar Kaduna, ta magantu kan maganar Mita wutar lantarki, inda tace kyauta ne.

Hukumar Kaduna Electric, tayi Kira ga kostomomi ta a fadin jihar Kaduna cewa su guje wa ‘yan damfara masu nema su basu kudi akan mitar wuta ko sanya wa.

Duk wanda ya tambaye ku kudi ko daga cikin ma’aikaci mu ko masu Musa sanya mita da su gaggauta kawo karan su ga kampani.

Shugaban ban gare mita na sashin Kaduna Electric, Eng. Aliyu Mohammed Gana, ya bayana haka a wata sanarwa da ya fitar a karshen mako ” ya bukace kostomomi da dukan Jama’a da kada su bada ko ficika akan mita karkashin tsarin raba mita na baidaya (NMMP) National Mass Metering Programme a turance, domin kuwa mita a karkashin shirin kyauta ne.

Sanan ya bukaci da a kawo qara duk wani ma’aikaci ko masu saka mita da ya bukaci a basu kudi ga kamfani.

Gana, yakara da cewa akwai bukatar mutane da ba su samu mita ba da su kara hakuri domin ana gudanar da raba mita a a tsari da matakai, wanda yanzu haka mungama da mataki 0, zakuma mufara da mataki 1 da zara Gwamnati ta bamu umarni.

Yace duk kostoma da ba zai iya jira ba har yasamu mita akar kashin Shirin NMMP zai iya nema mita akar kashin Shirin MAP, ama ba kyauta bane zai biya.

Zafafa Labarai