Countdown
Connect with us

Tsaro

Mazauna Rijana, Akilbu da Katari sun roki Gwamnatin Jihar Kaduna ta janye qudirin tayar dasu

Published

on

Garuruwa uku dake kan titin Abuja zuwa Kaduna da suka hada da Rijana, Akilbu da Katari, sun roki Gwamna Jihar Kaduna, Elrufai akan yayi hakuri kada ya tayarda da su daga garuruwan su.

A ranar 19 ga watan Mayu, 2022 ne Gwmana Jihar Kaduna, Elrufai ya bayanar dacewa akwai bukatar tayarda garuruwan sabida sun kasance mabuyar ‘yan ta’ada da masu basu rahoto.

Magaji Danjuma-Katari, Ciyama na unguwannin shine yayi rokon yayin zantawa da manema labarai, jiya a Kaduna.

Yace “A iyakar saninmu, al’ummominmu ba su san shigar kowane memba namu, kai tsaye ko a kaikaice, a duk wani lamari da za a iya tabbatar da shi a matsayin me aiki da ‘yan bindiga a ciki da wajen al’ummarmu. Don haka zarge-zargen dake cewa muna hada kai da ’yan bindiga, na boge ne Kuma shirme ne mara tushe.

Ya ce, “Sabanin labaran da ba su dace ba daga majiyoyi masu tambaya da kuma dillalan labarai na bangare daya, mazauna wadannan al’ummomi da dama sun kasance suna fuskantar matsalar ‘yan bindga,” in ji shi.

Ya bayyana cewa akwai wata babbar hanyar shanu da ta taso daga yankin Arewa ta tsakiya kuma ta ratsa babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna a wani wuri da ke kusa da Katari, wanda hakan ya ke bawa ‘yan bindiga dama su rika kai hare-hare.

Ya bukaci Gwamnati da ta hada hannu da hukumomin gwamnati da masu ruwa da tsaki a cikin al’umma, domin samar da hadin kai a yaki da ‘yan bindiga a yankin.

Danjuma-Katari ya kuma bukaci gwamnati da ta yi nazari cikin hikima tare da bin diddigin duk rahotannin tsaro da suka shafi al’ummomin, don tabbatar da cewa ba wai kawai hasashe ba ne.

Yakara dacewa Gwamnati ta hukunta duk wani mazauni yankin mu da aka tabatar yanada hanu a aiki tare da ‘yan bindiga kamar yadda doka ya tanada.

Ya ba da shawarar cewa yakamata jami’an tsaron da a ke turowa yankin mu, su kasance an basu isasun kayan aiki yadda ya kamata tare da zaburar da su domin tunkarar kalubalen da ake fuskanta.

“Daukar karin mambobin matasan mu cikin harkan jami’an tsaro domin karfafa manufar aikin ‘yan sanda ta hanyar samun amincewar al’umma, zai taimaka matuka.

Ya jaddada cewa, “Akwai bukatar haɓaka matsayin ilimi na al’ummomi. Sanan a samar da wani karin sashin ‘yan sanda domin karbar kararrakin a karamar hukumar Chikun dake kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna.”

Zafafa Labarai